IQNA

Za A Bude Masallatai 300 A Cikin Mako Guda A Kasar Masar

23:50 - May 01, 2019
Lambar Labari: 3483595
Bangaren kasa da kasa, a cikin wannan mako ne ake sa ran zaa bude masallatai guda 300 a fadin kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na dira ya hbarta cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’ikatar kula da harkokin addini a kasar Masar, ya jagoranci bude wani babban masallaci a garin Hira, tare da halartar sheikh Zakariya Alkhatib.

Wannan taron dai an gudanar da shi a karon farko bude wannan babban masallaci wanda aka sake gyara gininsa, wanda ya kai fadin mita 1200, sai kuma tsabar kudin da aka kashe wajen gyaransa da suka kai fan na kasar Masar miliyan 15.

Ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta ya bayyana cewa, suna da shirin bude masallatai 300 daga na zuwa watan azumin Ramadan mai alfarma, inda za a kammala aikin bude sabbin masallatan a cikin mako guda mai zuwa.

3808142

 

 

captcha