IQNA

Ministan Awkaf na Masar: Tsayawa tsaka-tsaki cikin lamarin addini shi ne wajabcin duniya ta yau

13:37 - April 27, 2023
Lambar Labari: 3489048
Tehran (IQNA) Ministan Awkaf na Masar ya jaddada wajabcin kiyaye daidaiton addini da kuma ajiye bambance-bambance a gefe daya a matsayin wajibcin duniya a yau.

A rahoton Bawabe Veto, Muhammad Mukhtar Juma, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar Masar, a wata ganawa da kungiyar dalibai ‘yan kasashen waje da suka haddace kur’ani mai tsarki, kuma suke da hazaka a fannin wakokin addini, kan muhimmancin himma wajen neman ilimi don yi wa addini hidima da kuma muhimmancin kiyaye daidaiton addini, kuma Ya jaddada nisantar duk wani nau'in tsaurin ra'ayi.

Ministan ya bayyana wadannan kalamai ne a wajen bude sansanin horas da daliban kasashen waje sashe na 18 a sansanin Abu Bakr al-Sadiq da ke birnin Iskandariyya.

Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar ce ta kafa wannan sansani.

A cikin wannan biki, ya bai wa daliban kasashen waje kwafin littafin “Al-Mukhtasar al-Shafi fi al-Ayman al-Kafi” inda ya ce an hada wannan littafi ne da nufin saukaka asasi na ilimin imani, dukkanin batutuwan da ke jawo cece-kuce, domin a duniyar yau, kiyaye daidaiton addini da nesantar tsattsauran ra'ayi da bambance-bambance masu tayar da kayar baya abu ne mai matukar muhimmanci.

 

 

 

4136682

 

 

captcha