IQNA

Littafan Turanci Da Suka Shafi Kur’ani A Baje Kolin Kasa da Kasa Na Kur’ani

17:49 - April 18, 2022
Lambar Labari: 3487187
Tehran (IQNA) Cibiyar A’immatul Huda (AS)  ta halarci bikin baje kolin kur’ani mai tsarki karo na 29 a dakin taron na Tehran inda ta yi rangwamen littafai na koyar da harshen turanci da ma’anonin kur’ani.

Shugaban cibiyar A’immatul Huda (AS)  a rumfar kayan dijital da littafan addini a baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 29 a  Tehran, Hossein Radmard ya ce: Ana bayar da muhimmanci ga koyan kur’ani da kuma koyar da ilimin kur’ani mai tsarki,a  akn haka an yi rangwamen kashi 85%.

Radmard ya bayyana cewa: Wannan shirin ya hada da horarwa a aikace na tsarin nahawu, sanin hanyoyin fahimta, koyar da kalmomi masu amfani dubu, fayil din da ake bukata don nahawu na asali, wanda aka gabatar a cikin fayilolin horarwa guda 75 a cikin surar Zumr.

Har ila yau shugaban cibiyar A’immatul Huda (AS)  ya bayyana cewa: Masu sha'awar suna iya duba shafin yanar gizon na Whiteboard wato  "Wboard.ir" don siyan wannan kunshin ta hanyoyi biyu na saukewa da aikawa ta flash.

Ya kamata a lura da cewa, baje kolin kur'ani mai tsarki karo na 29  na kasa da kasa a birnin Tehran mai taken "Qur'ani; Littafin "Bege da Aminci" ya fara ne daga ranar 17 ga watan Afrilu a babban masallacin Tehran kuma zai ci gaba har zuwa ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara.

Har ila yau, za a iya duba wasu daga cikin ayyukan baje kolin ta wannan shafi  iqfa.ir.

 

https://iqna.ir/fa/news/4050252

captcha