Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Shorouk cewa, a wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin kyauta ta kasar Aljeriya ta fitar, ta ce za a gudanar da gwajin matakin ne domin halartar gasar kur'ani mai tsarki ta kasar da za a yi a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilun 2022 .
Takardun da ake bukata don wannan jarrabawar sun hada da takardar haihuwa, takardar haddar Alkur'ani da aka yi shekara 2, da hotuna guda biyu da kuma bukatu a rubuce wanda sai a gabatar da su kafin ranar 13 ga Afrilu.
Za a gudanar da wannan jarrabawar ne a tsakanin cibiyoyin kur'ani da makarantun Al-Boyerieh, Tizi Wazu, Batnah, Qastanineh, Mileh, Gholizan, Telmsan, Saeededeh, Sukra, Al-Aghwat, Tamnafst, An Saleh da Alizi.