IQNA

Hamas: Matsayar Aljeriya Na Kin Amincewa Da Kulla Alaka Da Isra’ila Abin Alfahari Ne Ga Al'umma

18:24 - November 13, 2021
Lambar Labari: 3486551
Tehran (IQNA) Hamas ta yi maraba da kalaman ministan harkokin wajen kasar Aljeriya kan kin amincewa da daidaita alaka da Isra'ila.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa,

Shugaban reshen siyasar kungiyar Hamas a kasashen waje ya yi maraba da kalaman ministan harkokin wajen kasar Aljeriya na kin amincewa da daidaita alaka da Isra'ila.

Shugaban bangaren siyasar kasashen waje na kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa, a  Kungiyar Hamas mun yi maraba da kalaman ministan harkokin wajen Aljeriya Ramat Lamara, wanda ya soki sabon yunkurin da ake yi a yankin na daidaita alaka da gwamnatin mamaya, tare da yin kakkausar suka ga duk wani mataki na wasu gwamnatocin larabawa da ke hankoron kulla hulda dagwamnatin yahudawa.

Sami Abu Zuhri ya kara da cewa: Mu a kungiyar Hamas muna alfahari da irin wadannan kalamai na Aljeriya, muna kuma bayyana goyon bayanmu gare su, domin wadannan kalamai na kawo cikas ga yunkurin mamaye yankunan Larabawa da yahudawan Isra'ila ke yi, musamman ma a nahiyar Afirka da Isra’ila ke kokarin kutsawa a yanzu.

Wasu daga cikin kasashen larabawa a cikin lokutan baya-bayan nan sakamakon matsin lamba daga Amurka da Saudiyya, suna karkata ga kulla alaka da Isra’ila, daga cikin wadanda suka mika kai ya zuwa yanzu dai har da UAE, Bahrain, Sudan da kuma Morocco, yayin da kuma wasu suke ci gaba da fuskatar matsin lamba kan hakan, amma suna ci gaba da yin turjiya.

 

4012693

 

captcha