IQNA

An Rusa Majalisar Dokokin Kasar Iraki

22:29 - October 07, 2021
Lambar Labari: 3486398
Tehran (IQNA) shugaban majalisar dokokin kasar Iraki ya sanar da rusa majalisar a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben kafin wa'adi.

Shafin yada labarai na mdeast.news ya bayar da rahoton cewa, Muhammad alhalbusi shugaban majalisar dokokin kasar Iraki ya sanar da rusa majalisar bisa dokar da aka kafa a ranar 31 ga watan Maris 2020, wadda ta bayar da damar yin hakan idan za a yi zaben kafin wa'adi.

Rahotanni daga kasar ta Iraki na cewa an tsaurara matakan tsaro a sassan daban daban na kasar, gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da za’a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.
 
Zaben da aka kira na kafin wa’adi, an kira shi ne da zumar biya bukatun masu boren da ya barke a watan Oktoban 2019.
 
Masu zanga zangar a wancan lokacin wandanda mafi akasarinsu matasa ne sun koka ne kan cin hanci da rashawa da rashin aikin yi.
 
Bayanai sun ce gabanin zaben an karfafa matakan tsaro ta hanyar jibge jami’an tsaro a kasar dake fama da matsaloli na tsaro masu nasaba da kungiyar daesh.

4002950

 

 
captcha