IQNA

Ana Tarukan Juyayin Shahadar Imam Ridha (AS) AKasar Canada

19:34 - October 07, 2021
Lambar Labari: 3486396
Tehran (IQNA) mabiya mazhabar Ahlul bait suna gudanar da tarukan juyayin shahadar Imam Ridha (AS) a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamar kowace shekara a bana ma mabiya mazhabar Ahlul bait suna gudanar da tarukan juyayin shahadar Imam Ridha (AS) a kasar Canada.

Taron wanda aka gudanar a yau, ya hada da tunawa da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW) da kuma shahadar Imam Hassan (AS) wanda ya kasance a ranar Litinin da ta gabata, sai kuma shahadar Imam Ridha (AS) wanda ya yi daidai da ranar yau Alhamis.

An dai gudanar da tarukan ne a babban ginin cibiyar musulmi da ke Jihar Alborta a kasar ta Canada, wanda kuma taron ya gudana ne bisa tsari na kiwon lafiya wanda hukumomin jihar suka sanar.

A kowace shekara dai ana gudanar da irin wadannan taruka a wannan cibiya da ma wasu cibiyoyin a wasu jihohin kasar ta Canada.

 

 

4002934

 

 

captcha