IQNA

Masar Ta Rufe Masallacin Zainab Da Ke Birnin Alkahira

22:36 - September 04, 2021
Lambar Labari: 3486271
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Masar ta rufe masallacin Sayyida Zainab da ke birnin Alkahira a yau saboda dalilai na kiwon lafiya.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a yau gwamnatin kasar Masar ta rufe masallacin Sayyida Zainab da ke birnin Alkahira saboda dalilai na kiwon lafiya.

Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, tun kafin wannan lokacin an bayar da sanarwa ga masu kula da wannan masallaci kan daukar matakan kiwon lafiya, amma ba su kula ba, saboda haka daga karshe dai an rufe masallacin sai abin da hali ya yi.

Tun bayan bullar cutar corona wannan masallaci yana daga cikin masallatai na farko da aka fara rufewa, kafin daga baya aka bude shi.

Ana danganta wannan wuri ne dai Sayyid Zainab amincin Allah ya tabbata a gareta diyar Fatima Zahra (AS) diyar manzon Allah (SAW) inda wasu ke cewa a tarihi bayan kisan Imam Husssain (AS) da zuriyar manzon Allah (SAW) da sojojin Yazid dan Mu'awiya suka yi a Iraki, a lokacin da za a kai su Zainab zuwa fadar Yazid a Sham, sun yada zango a Masar, yayin da wasu ke cewa ta rasu a Masar, amma dai ingantattun ruwayoyi sun tabbatar da cewa ta rasu ne a Damascus.

 

3994991

 

 

captcha