IQNA

An Sanar Makoki Na Kwaki Bayan Mutuwar Mutuwar Mutane Sakamakon Gobara A Iraki

23:49 - July 13, 2021
Lambar Labari: 3486103
Tehran (IQNA) a kasar Iraki an ayyana zaman makoki na kwanaki 3 bayan gobarar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da tamanin a wani asibiti.

Mutane akalla 83 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin 100 suka jikkata a wata gobara da ta tashi a wani asibitin kula da masu cutar Korona dake lardin Dhi Qar dake kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar INA ya ruwaito cewa, gobarar ta tashi ne da yammacin jiya a cibiyar kebe wadanda suka kamu da cutar corona ta asibitin al-Hussein da ke birnin al-Nasiriyah.

Ofishin yada labarai na firaministan Iraqi, Mustafa al-Kadhimi, ya sanar da cewa, firaministan ya kira wani taron gaggawa da ya kunshi wasu daga cikin ministoci da shugabannin tsaron kasar, domin tattaunawa kan asarar da gobarar ta haifar.

Wannan ba shi ne karon farko ba da irin hakan take faruwa a kasarta Iraki ba, don kuwa ko a watan Afrilu, fashewar wata tukunyar iskar gas na oxygen wanda ya jawo gobara da ta yi sanadin mutuwar mutum 82 tare da jikkata 110 a wani asibiti a Bagadaza babban birnin kasar, lamarin da ya sanya ministan lafiya na kasar a lokacin Hassan al-Tamimi ya yi murabus.

3983715

captcha