IQNA

Kwamitin Malaman Musulmi A Aljeriya Ya Bukaci Kai Taimakon Gaggawa Ga Musulmin Rohingya

17:02 - March 25, 2021
Lambar Labari: 3485763
Tehran (IQNA) kwamitin malaman musulmin kasar Aljeriya ya bukaci kai daukin gaggawa ga musulmin Rohingya da gobara ta kone sansaninsu.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, sakamakon gobarar da ta auku a cikin sansanin ‘yan gudun hijira na musulmin Rohingya a Bangaladesh, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 40 da jikkatar wasu da dama, kwamitin malaman musulmin kasar Aljeriya ya bukaci kai daukin gaggawa ga musulmin na Rohingya da gobara ta shafa.

Karim Rizqi shi ne shugaban bangaren kula da harkokin kasa da kasa na kwamitin malaman musulmi a kasar Aljeriya, ya kuma bayyana cewa suna bukatar gwamnatin Aljeriya ta bayar da damar kai agaji ga wadannan musulmi da ibtila’in ya auka musu.

Ya ce a shirye suke su bayar da agajin gaggawa ga wadannan bayin Allah, kuma hakan nauyi ne da ya rataya kan dukkanin musulmi da su taimaka ma ‘yan uwansu a duk inda suke, kasantuwar suna cikin matsananciyar bukatar taimako.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, taimakon da kwamitin malaman musulmin kasar Aljeriya ke shirin bayarwa zai shafi bangaren samar da abubuwan bukatar rayuwa ne na gaggawa, wanda kuma suna jiran matakin da gwamnatin Aljeriya za ta dauka na taimakawa domin aikewa da taimakon.

 

3961095

 

 

captcha