IQNA

WHO: Madina Na Daga Cikin Birane Mafi Aminci Ta Fuskar Kiwon Lafiya A Duniya

22:55 - January 28, 2021
Lambar Labari: 3485598
Tehran (IQNA) hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa birnin Madina mai alfarma yana daga cikin birane mafi lafiya a duniya.

Shafin yada labarai na Arab News ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa birnin Madina mai alfarma yana daga cikin birane mafi lafiya a duniya.

Wannan na zuwa biyo bayan wata ziyarar rangadi da jami'an hukumar lafiya ta duniya suka kai birnin Madina ne, domin ganin yadda ake kula da lamurran tsafta da sauran harkoki na kiwon lafiya.

Jami'an sun fitar da bayani da ke cewa, ana daukar mtakan da suka dace na tsafta yadda ya kamata, wanda hakan yasa birnin yana daga cikin birane da ake kula da kiwon lafiya yadda ya kamata.

Birnin Madina wanda a nan masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka, yake wanda yake samun maziyarta a kowace rana, yana daga cikin wurare da suka samun cunkoson jama'a a.

3950420

 

captcha