IQNA

Habasha Da Isra’ila Na Tattauna Batun Hijirar Yahudawan Ethiopia Zuwa Isra’ila

22:59 - December 02, 2020
Lambar Labari: 3485423
Tehran (IQNA) Ministar Isra’ila mai kula da yahudawa masu hijira zuwa daga kasashen duniya zuwa Falastinu da yahudawa suka mamaye ta isa Habasha.

Ministar Isra’ila mai kula da yahudawa masu hijira zuwa daga kasashen duniya zuwa Falastinu da yahudawa suka mamaye ta isa Habasha, domin tattauna batun hijirar yahudawan Habasha zuwa Falastinu da yahudawa suka mamaye.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Penina Tamanu Shata, Ministar Isra’ila mai kula da yahudawa masu hijira zuwa daga kasashen duniya zuwa Falastinu da yahudawa suka mamaye, isa birnin Addis Ababa na kasar Habasha, domin ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar.

Manufar ziyarar dai ita ce tattauna batun bayar da dama ga wasu daga yahudawan Ethiopia, domin su yi hijira zuwa Isra’ila, inda gwamnatin yahudawan ta sanar da cewa, ta bayar da dama ga yahudawan Habasha 2000, domin su koma Isra’ila.

Miministar gwamnatin yahudawan wadda ita ma ‘yar asalin kasar Habasha ce, ta gana da firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad Ali kan wannan batu, inda ta ce sun ware makudaen kudade domin taimaka ma ‘yan Habasha mazauna Israila.

 

3938507

 

captcha