IQNA

Littafin Injila Mai Dauke Da hotuna Na Farko A Kasar Habasha

22:54 - October 06, 2020
Lambar Labari: 3485251
Tehran (IQNA) an samu littafin Injila na farko da aka rubuta shi tare da hotuna.

Wanan littafi yana ajiye ne a ckin duwatsun Garima da ke kasar Habasha, wanda manyan malaman kiristoci sun san da shi, kuma suna girmama shi da wurin da aka ajiye shi.

Wanann dai yana daga cikin dadaddun abubuwa na tarihi a duniya, wanda wasu daga cikin littafan daka rubuta tsawon daruruwan shekaru kafin bayyanar muslucni sun bayani kan wannan littafi, da kuma inda aka ajiye shi a kasar Habasha.

Littafin dai yana dauke da rubutun matanin Linjila, a daya bangaren kuma yana dauke da hotuna na abin da matakin ke bayani da aka zana su, kuma an rubuta littafin ne akan fatar akhabashauya.

Yanzu haka dai littafin yana nan inda aka ajiye shi a cikin wani daki akan tsaunukan Garima  a cikin kasar Habsha, kuma kwafi biyu ne na littafin ajiye a  cikin dakin.

Ma’ikatar raya al’adu ta kasar Habasha taa niyayr gina wani wuri na musamman wanda yafi aminci, domin ajiye wanna littafi, ta yadda hatta masu yawon bude ido za su iya zuwa wurin ganinsa.

 

3927657

 

 

 

 

captcha