IQNA

An Dakatar Da Sallar Jum'a Tsawon Makonni Uku Masu Zuwa Saboda Corona

21:01 - September 16, 2020
Lambar Labari: 3485190
Tehran (IQNA) an dakatar da gudanar da sallar Juma'a har tsawon makonni uku masu zuwa saboda yaduwar cutar corona.

Jaridar Quds arabi ta bayar da rahoton cewa, Hatam Abdulkadir mamba a kwamitin kula da harkokin masalacin Quds ya bayyana cewa, saboda yaduwar cutar corona an dakatar da gudanar da sallar Juma'a har tsawon makonni uku masu zuwa.

Bayanin ya ce an dauki wannan mataki ne bayan masana kan harkokin kiwon lafiya suka yi la'akari da karuwar kamuwa da cutar corona a birnin.

Mutane 8000 ne suka kamu da cutar corona daga watan Yulin da ya gabata zuwa yanzu, inda a yanzu mutane 2000 ne suke fama da cutar.

3923477

 

captcha