IQNA

Taro Kan Hakkokin Mata A Mahangar Musulunci Da Kiristanci A Habasha

20:50 - March 03, 2018
Lambar Labari: 3482447
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taron karawa juna sani kan hakkokin mata a mahangar addinin musulunci da kuma addinin kiristancia kasar Habasha.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adun musulunci cewa, shugaban ofishin yada aladun musulunci na Iran a kasar Habasha Sayyid Hasan Haidari ya gudanar da wata tattaunawa tare da shugaban bangaren nazarin addinai na jami'ar Addis Ababa.

Babbar manufar wannan ganawa dai ita ce samar da hanyoyi na kara karfafa fahimtar juna tsakanin mabiya addinain kiristanci da musulunci a kasar ta Habasha da ma dukkanin yankuna na gabashin nahiyar Afirka.

Dukaknin bangarorin biyu dai sun cimma matsaya kan shirya wani taron karawa juna sani kan mahangar addinan musulunci da kiristanci a kan hakkokin mata.

Za a gudanar da taron ne na hadin gwiwa da jami'ar Addis Ababa da kuma karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar.

Za a gayyaci manyan malamai da masana da za su gabatar da makaloli da kasidu a wurin taron.

3696408

 

 

 

 

captcha