IQNA

Palastine: Kasashen Afirka Su Tsayin Daka Wajen Bijirewa Kudirin Trump

22:19 - January 28, 2018
Lambar Labari: 3482342
Bangaren kasa da kasa, jami’an gwamnatin Palastine sun bukaci kasashen Afirka da su ci gaba da yin tsayin daka kan wajen bijirewa Trump kan batun Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo spotink cewa, a cikin wani sako da jami’an gwamnatin Palastine suka aikewa taron shugabannin kasashen Afirka sun bukaci da su ci gaba da yin tsayin daka kan wajen bijirewa Trump kan batun Quds da ma sauran batutuwa da suka shafi hakkokin palastinawa.

Wannan wasika tana zua a daidai lokacin ad shugabannin Afirka suke fara taronsu a yau a binin Addis Ababa na kasar habasha, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suke ci ma nahiyar tuwo a kwarya.

Gwamnatin palastine ta yi amfani da wannan damar domin jaddada rokonta ga kasashen Afirka kan suci gaba da mara mata baya wajen kin amincewa da matakan zalunci da danniya da sabuwar gwamnatin Amurka take dauka wajen baya da dukkanin taimako ga gwamnatin yahudawan sahyuniya.

Baya ga haka ma a kwanain baya shugaban Amurka Dnad Trump yay i kamalan batunci a kan musulmi da kuma kasashen Afirka, inda ya bayyana su da wuirkalakantattu, tae da bayyana al’ummomin Airka a matsayi shara ko bola.

Wannan lamari dai ya bakantawa da dama daga cikin kasashen Afirka masu ‘yancin siyasa, har ma da wadanda suke yi wa Amuka a amshin shata.

3686131

 

captcha