IQNA

Babban Taron Kiristoci Mabiya Darikar Katolika A Ghana

16:56 - November 28, 2017
Lambar Labari: 3482148
Bangaren kasa da kasa, manyan malaman mabiya addinin kirista a kasar Ghana sun gudanar da babban taronsu na shekara-shekara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wannan makon ne manyan malaman mabiya addinin kirista akasar Ghana sun gudanar da babban taronsu na shekara-shekara inda ake tattauna lamurra da suka shafi zamantakewar jama'a.

Wanann taron dai yak an mayar da hankali ne kan batutuwa da suka shafi zamantakewa da kuma duba irin matsalolin da ake fuskanta da yadda za a magance su.

Daga cikin abubuwan da taron yake yin dubi a kansa har da tarbiyar matasa da kuma yadda za a tabbatar da cewa ba su lalace ba, musamman yadda ake samun shigar al'adun waje a cikin al'umma inda matasa kuma su ne sukan yi sautrin daukar sabbin dabiu.

Kiristocin kasar Ghana suna da kyakyawar alaka da musulmi, ta yadda sukan gayyaci musulmi wajen halartar wadannan taruka, domin musulmi su bayar da nasu shawarwarin kana bin da ya kamata yi domin tabbatar da cewa al'umma ta zauna lafiya da kuam ci gaban kasa da tarbiyantar da yara bisa kyawawan dabiu.

3667611


captcha