Ya ci gaba da cewa, makarantun muslunci suna fuskantar matsaloli a kasar musamman a cikin shekarun baya-bayan nan, inda malamai da suke koyarwa suke janye jikinsu, bisa hujjar karancin albashi.
Y ace wannan ya nuna cewa akwai bukatar yin wani garambawul a harjar tafiyar da makantun muslunci a kasar, ta yadda za su zama daidai da sauran makarantu ta fuskar inganci da kuma daukar nauyin jami'a da kuma malamai.
A lokutan baya cibiyoyin muslunci ne dai suke daukar nauyin makarantunci muslunci, amma daga bisani daukar nauyinsu da kuma tafiyar da su ya koma akan wuyan gwamnati, duk kuwa da cewa musulmi ne suke nauyin yin tsare-tsaren tafiyarwa.