IQNA

MDD Ta Ce Akwai Yiwuwar Dakatar da Taimakon Abinci Ga Palastinawa

23:54 - June 14, 2017
Lambar Labari: 3481611
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta yi garrgadin cewa akwai yiwuwar a dakatar da bayar da agajin abinci ga wasu Palastinawa saboda karancin kudi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalti daga shafin yada labarai na Arab 48 cewa, hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, tana fuskantar matsaloli dangane da ayyukan da take gudanarwa a Palastinu ta fuskar ciyar da wasu Palastinawa masu fama da matsalar talauci a Gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.

Kakakin majalisar dinkin duniya Stéphane Dujarric ya bayyana cewa, sakamakon rashin bayar da kudade daga kasashen duniy, hakan ya sanya kimanin palastinawa dubu 150 za su rasa taimakon abinci na majalisar dinkin duniya da suke samu, inda y ace abin da ake bukata domin cike wannan gibi shi ne dala miliyan 6.6 a halin yanzu.

3609709


captcha