IQNA

Dakushe Zuciyar Matasa Kan Ilmi Na Ci Gaban Alumma Babban Cin Amanar Kasar Ne

22:41 - October 14, 2015
Lambar Labari: 3385727
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci ya jaddada wa jami’an gwamnati cewa, ci gaba n da Iran ta samu a dkkanin bangarori na nukiliya da sauran gaskiya ne, kuma dakushe zukatan matasa kan kara himma babban cin amana ne ga kasa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto tarjamar bayanin ganawar ta jagora daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora da ke cewa, a safiyar yau Laraba ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu gungun daliban jami'a da wadanda suka nuna bajinta a bangarori daban-daban na ilimi na kasar Iran, inda yayi karin haske kan wasu lamurra bugu da kari kan nasihohi da kuma jan kunne da masanan da kuma jami'an cibiyar da ke kula da masana ‘yan baiwan. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Lalle makomar kasar nan, bisa la'akari da manufofi, take, yunkuri na juyin juya hali a tsakanin al'umma da kuma irin rawar da matasa masana suke takawa cikin gagarumin yunkuri na ilimi da ke gudana a kasar Iran, lalle makoma ce mai kyaun gaske, ci gaba, tsayuwa da kafa da kuma tasiri a fagage na yankin nan da kuma duniya. Ko shakka babu wadanda a halin yanzu suke kokarin kashe gwuiwan matasa dangane da rayuwarsu ta yau da kuma makomarsu, lalle sun aikata babban laifi da cin amanar kasa.
Tun a farkon jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin kwazo da fahimtar da matasan suke da ita inda ya ce: A yayin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take dogaro da irin karfin da take da shi na cikin gida, don haka ana ganin wadannan matasa masu kwakwalwa da fahimta a matsayin mafi girman dama da kuma arziki na kasa da ake da shi.
Bayan ‘yar wannan gajeruwar gabatarwa, Ayatullah Khamenei ya gabatar da wasu nasihohi irin na mahaifi ga wadannan matasa masana. Daukar irin wannan ilimi da fahimta ta koli da ake da ita a matsayin wata ni'ima ta Ubangiji wacce kuma ta cancanci godiya ga Allah, ita ce nasiha ta farko da Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi wa masana matasan inda ya ce: Har ila yau kuma yana da kyau ku dauka cewa wannan irin ilimi da fahimta da kuke da ita ta samo asali ne albarkacin wannan juyin juya halin Musuluncin, don kuwa wannan juyin ne ya samar wa matasan Iran da mutumci da kuma jaruntakar fitowa fili wajen amfani da irin wannan kwarewa ta cikin gida da suke da ita.
Ayatullah Khamenei ya bayyana samun matsayin ilimi na sama a tsakanin kasashe ashirin na duniya a matsayin daya daga cikin albarkokin juyin juya halin Musuluncin inda ya ce: A halin yanzu kasar Iran ta kai wani matsayi na koli na ilimi, duk kuwa da irin matsaloli da suka hada da kallafaffen yaki, matsin lamba na siyasa da takunkumi na tattalin arziki da ta fuskanta tsawon shekaru talatin din da suka gabata.
Don haka sai ya kirayi matasan da cewa: Har ila yau kuma wannan matsayin na koli na ilimi da kuka samu, kun same shi ne albarkacin irin tsaron da kasar nan take da shi. A saboda haka wajibi ne ku gode wa wadanda suke tabbatar da wannan tsaron mutane irin su Shahid Janar Hamedani (daya daga cikin kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran da yayi shahada a kasar Siriya cikin ‘yan kwanakin nan).
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin gagarumar jana'izar da aka yi wa shahid Janar Hamedanin musamman a garin Hamedan a matsayin wata alama ta nuna godiya da kuma jinjinawar al'ummar Iran ga masu tabbatar musu da tsaronsu inda ya ce: Matukar babu tsaro, to kuwa ba za a samu damar bincike na ilimi, karatun jami'a da kuma ci gaban ilimi ba.
Fifita ruhi na kokari bisa ruhin cin na bulus ita ce nasiha ta biyu da Ayatullah Khamenei yayi wa matasa masanan.
Jagoran ya bayyana cewar daya daga cikin bala'oin da suke fuskantar mutanen da suke da wani fifiko a wani bangare shi ne ‘irin wannan yanayi na sakaci da nuna kai' inda ya ce: Wannan wata cuta ce, wacce bai kamata ku bari ta girma ba. Hanya guda kawai ta fada da ita, ita ce karfafa ruhin kokari da aikata ayyuka da dukkan karfi saboda Allah a matsayin wani nauyi na shari'a da ke wuyan mutum.
Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa shiga cikin irin ziyarar da ake kai wa kauyuka da karkara don gane wa idanuwa abubuwan da ke faruwa a can a matsayin wata hanyar ta daban ta karfafa ruhin kokari da son aiki, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Shiga cikin irin wadannan tafiye-tafiye ya kan sa mutum ya samu masaniya kan sauran al'ummomi da irin matsalolin da ake fuskanta.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan irin masaniya da kwarewar da yake da ita ta shekara da shekaru bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Khamenei ya bayyana rashin masaniyar matsalolin da ake fuskanta a wasu yankuna na kasar Iran da wasu jami'an gwamnati suke da ita a matsayin babbar matsala. Daga nan sai ya ce: Irin wadannan tafiye-tafiye wata babbar dama ce ga matasa ta su sami matsaniya kan halin da ake ciki da kuma yin hidima kai tsaye ga al'umma.
Nasiha ta uku da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa matasa masanan ita ce kokarin ci gaba da zama a cikin kasa bayan sun gama karatunsu don yin hidima ga kasar su maimakon tafiya wata kasa ta waje da tunani wai za a sami jin dadi da saukin rayuwa. Jagoran ya bayyana cewar: Maimakon ku sa kanku cikin irin wannan yanayi na rashin tausayi da imani da ake fuskanta a kasashen wajen, ku zamanto masu tsara kasarku da kuma ciyar da ita gaba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ci gaba da zama a kasarku da kokari wajen magance matsalolin da ake fuskanta, lalle hakan wani lamari ne abin jinjinawa da kuma daukaka.
Nasiha ta hudu da Ayatullah Khamenei yayi wa matasan ita ce rashin razana da rusuna kai ga irin ci gaban da aka samu a kasashen yammaci inda ya bayyana musu cewa: Duk kuwa da cewa kasashen yammaci sun sami ci gaba mai yawan gaske a fagen ilimi da fasaha, to amma bai kamata a razana da kuma mika kai ga hakan ba. Don kuwa irin karfin da matasan Iran suke da shi, wani karfi ne mai girman gake. Idan har abin kwatantawa ne, to za a kwatanta irin ci gaban da Iran ta samu a halin yanzu ne bayan shekaru talatin da nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma shekaru talatin din da wadancan kasashen suka sami ‘yancin kansu.
Ayatullah Khamenei ya ce matasa masanan na Iran za su iya kai wa ga kololuwa ta ilimi bisa la'akari da irin karfi da kwarewar da suke da ita.
Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi cibiyar da take kula da lamurran masana matasan da su ci gaba da gudanar da tsare-tsare masu kyau wadanda suka dace wajen ganin an taimakawa matasan a dukkanin abin da suka sa a gaba na ci gaban ilimi, kamar yadda kuma ya kirayi matasan da su ba da himma wajen kirkiro sabbin abubuwa da kuma samar da hanyoyi na ilimi da za a magance matsalolin da ake fuskanta musamman a bangaren tattalin arziki.

 

3385433

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha