IQNA

An Gudanar Da Zaman Ta’aziyyar Wadanda Suka Rasu A Hadarin Mina

22:49 - October 04, 2015
Lambar Labari: 3379493
Bangaren siyasa, an gudanar da zaman makoki na mahajjatan da suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru a Mina a wajen aikin hajjin wannan shwekara tare da halartar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a Husainiyyar Imam Khomenei (RA)


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, a yau an gudanar da zaman makoki na mahajjatan da suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru a Mina a wajen aikin hajjin wannan shwekara tare da halartar jagoran juyin jya halin mslunci da kuma wasu daga cikin malaman addini da dangin wadanda suka rasu.

Haka nan kuma an gabatar da jawabai dangane da abion da ya faru da yadda wadanda bayin Allah suka samu shahada a wannan wri mai tsarki, wanda wasu masu barna suka yi amfani da ikon da suke da shi domin bata sunan addinin mulsunci a idon duniya ta hanyar aikata abin da suka aikata kan bakin ubangiji.

Wanda ya yi jawabi Hojjatol islam Saddighi ya bayyana cewa, Al Saud su ne suka jaza dukaknin abin da ya faru a Mina, kuma duk wani kokarin da za su yi domin wanke kansu daga barnar da suka aikata ba za su iya ba, domin duniya ta sheda abin da ya faru baki daya.

Wannan dai yana daga cikin abubuwa na ban takaici da suka taba faruwa  atarihin hajji a karkashin masarautar da ke rike da madafun iko a wannan kasa a halin yanzu, duk kuwa da cewa suna ta hankoron dora laifin hakan a kan wasu bangarori.

AQ daidai lokacion da ake gudanar da wannan zaman makoki a wannan Husainiya ta Imam khomenei (RA) ana gudanar da wasu makokan a hubbaren Sayyid Ma’asuma (SA) a birnin Qom da ma wasu garuruwan na daban.

3379461

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha