IQNA

Kisan Musulmi A Afirka Ta Tsakiya Yunkuri Ne Share Su Daga Kasar

18:15 - February 24, 2014
Lambar Labari: 1379469
Bangaren siyasa, kisan musulmi da ake yi babu ji babu gani a jamhuriyar Afirka ta tsakiya wani sabon yunkuri ne na share musulmin da suke cikin kasar baki daya tare da mayar das u 'yan gudun hijira ko mkuma wadanda ba su da wata makoma a kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai da kula da hulda da jama'a a babbar cibiyar Ahlul bait ta duniya cewa, a cikin bayanin da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa kisan musulmi da ake yi babu ji babu gani a jamhuriyar Afirka ta tsakiya wani sabon yunkuri ne na share musulmin da suke cikin kasar baki daya tare da mayar da su 'yan gudun hijira ko kuma wadanda ba su da wata makoma a kasar a siyasance da sauransu.
'Yan bindiga mabiya addinin kirista a kasar Afirka ta tsakiya sun ce ba za su ajje makaman su ba matukar kungiyar 'yan tawajen saleka ba su ajje nasu makaman ba, kamfanin dillancin labarai na kasar Iran ya habarta cewa duk da irin Dakarun kasar Faransa na kasashen Afirkan da ke jibke a tsakiyar Afirka har yanzu sun kasa tabbatar da tsaron a wannan kasar inda matasan da ke dauke da makamai kiristoci a kasar suka ce ba za su ajje makamansu ba matukar kungiyar 'yan tawayen saleka suma ba su ajje na su makaman ba.
Rahotanin sun kara da cewa a karshe wannan Maku tsahin 'yan tawayen Saleka sun gudu daga Garin Bonkai inda suka tunkari arewacin kasar sandiyar shigar Sojojin Faransa da kasashen Afirka a wannan Gari, a bangare guda kuma dubu dubatan Al'umar kasar musulmi ne ke gudu hijra zuwa kasar Kamaru.

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cibiyar Ahlul Bait
captcha