IQNA

Paparoma Ya Gana Da Shugaban Falastinawa A Fadar Vatican

19:10 - November 05, 2021
Lambar Labari: 3486516
Tehran (IQNA) Shugaban Falasdinawa da Paparoma Francis shugaban kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya sun gana a fadar Vatican.

Shafin Vatican News ya bayar da rahoton cewa, Shugaban Hukumar Falasdinu Mahmoud Abbas da Paparoma Francis shugaban darikar kiristoci ta Katolika na duniya sun gana a fadar Vatican, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi bangarorin biyu.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka faru a baya-bayan nan a Falasdinu, da kuma yin ayyuka na hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunan Falasdinu da ma yankin gabas ta tsakiya.
 
Abbas ya kuma jaddada cewa halin da ake ciki a Falasdinu yana kara tabarbarewa yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri a kan al'ummar Falastinu.
 
Paparoma da Mahmoud Abbas sun kuma tattauna kan bukatar karfafa 'yan uwantaka da inganta zaman lafiya tsakanin addinai daban-daban a yankunan Falasdinu.
 
Paparoma Francis da Abbas sun kuma jaddada cewa, ya kamata kowa ya amince da birnin Kudus a matsayin wurin mu'amala, ba rikici ba, kuma ya kamata ya kiyaye matsayin birni mai tsarki ga dukkanin addinai uku, musulunci kiristanci da yahudanci, tare da tabbatar da samun mafita, da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Falastinu da ma duniya.
 
Shugaban hukumar Falasdinawa ya isa birnin Rome ne a wata ziyarar aiki da ya fara tun a ranar Litinin da ta gabata inda ya gana da shugaban kasar Italiya Sergio Matarella a ranar Laraba.
 

 

4010724

 

 
 
captcha