Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana damuwa kan halin da Abdulrahman Al-shawi yak e ciki.
Ya ce wannan dan shekaru 9 da haihuwa baya a matsayin wata barazana ga Isra’la, amma jami’an tsaro sun harbe shi da harsasai masu rai a garin Nablus.
Jami’in y ce suna bukatar ganin an gudanar da bincike na gaskiya kana bin da ya faru da wannan yaro, kuma a dauki matakai na hukunta wadanda suka aikata hakan.
A jiya ce sojojin Isra’ila suka bude wuta kan wannan karamin yaroa garin Nablus a lokacin da wasu matasa suke wani jerin gwanoa lokacin da yke tsayea gefen titi, a halin yanzu yana nan rai kwakwai mutu kwakwai.