IQNA

An Kafa Wuraren Karatun Kur’ani Akan Hanyoyin Isa Karbala

23:39 - November 03, 2017
Lambar Labari: 3482063
Bangaren kasa da kasa, an kafa wasu wurare na musamman a kan hanyoyin isa birnin karala na karatun kur’ani mai tsarki daga a kan hanyoyin Najaf da Babul.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama’a na hubbaren Alawi ya sanar da cewa, an kafa wasu wurare na musamman na karatun kur’ani mai tsarki a kan hanyoyin isa birnin Karala daga a kan hanyoyin Najaf da Babul masu yin tattakin ziyarar arbaeen.

Bayanin ya ce wadannan wurare sun kushi kwafi-kwafi na kur’ana da kuma wasu daga littafai na hukunce-hukunce karatun kur’ani mai tsarki.

Ana yin karatun a cikin jam’I kamar yadda kuma akan yi a daidaiku, duk wanda mutum yake bukata, kamar yadda kuma a kan saurari karatun masu harda.

Babbar manufar hakan da ita ce raya lamarin kur’ani a cikin wannan tattaki da masoya Imam Hussain (AS) suke yi zuwa karbala domin gudanar da ziyarar arbaeen.

Tun kafin wannan lokacin dai an fara gudanar da irin wannan taro na raya sha’anin kur’ani a lokacin tarukan ashura d kuma arbaeen, inda dubban mutane sukan shiga cikin wannan shiri na daukaka lamarin addini.

Mahukunta a Iraki sun ce ana sa ran adadin mutanen da za su halarci tarukan arbaeen abana zai yi yawan gaske, inda a shekarar da ta gabata adadin ya haura miliyan sha biyar.

3659538


captcha