IQNA

Adadin Masu Ziyara A Karbala Ya Kai Nawa?

21:13 - October 12, 2016
Lambar Labari: 3480848
Bangaren kasa da kasa, wani jami’I a Iraki ya bayyana cewa adadin mutanen da suka isa Karbala zumin gidanar da taron ashura ya hura miyan hdu da rabi.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Qais Muhammadawi babbn jami’in soji maikula da yankin Furat ya bayyana cewa, wannan adadi ya hada da masu ziyara na cikin Iraki ne da kuma wadsanda suka zo daga kasashen ketare.

Haka nan kuma ya kara da cewa adadin wadanda suka yi tafiyar tuwairij ya kai miliyan biyu, kuma tafiyar da suka yi zuwa cikin birnin karbalata kai ta sa’oi uku a jere.

Tafiyar tuwairij dai ana fara ta a lokacin Ashaura baya kiran sallar zuhur, kuma ana faraway daga yankin Kantaratu Salam, ana bi ta hubbaren Abbas (AS) zuwa hubbaren Imam Hussain (AS)

3537427


captcha