Dan ta’addan ya yi jigidar bama-bamai na dauri guda 9 da nufin tayar da su lokaci guda kan masu taron na Ashura, to amma da ikon Allah shirinsa bai yi nasara ba.
A cikin shekarun 2014 da 2015 an samu karuwar yawan kai harin ta’addanc a kan masu gudanar da tarukan ashura musammana kan hanyarsu ta isa birnin da hubbaren mai tsarki yake.
Masu kai harin dai suna da akidar kafirta musulmi ne musamman ma dai mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah, inda suke kiran hakan a matsayin jihadi.
‘Yan ta’addan dai suna samun dauki da goyon baya ne daga wasu kasashe da suke bas u kariya da kuma biyan malaman da suke wanke musu kwakwale domin kai irin wadannan hare-hare da sunan jihadi a tafarkin abin da suke kira sunna.