IQNA

Karatun Al-Qur'ani na Tsohon Dan wasan Arsenal

An yada wani bidiyon karatun ur’ani  “Wasiriki Abu Diabi” tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Bidiyon karatun “Wasiriki Abu Diabi” tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kasar Ingila, daga aya ta 1 zuwa ta 14 a cikin suratul Taha.

An haifi Wasiriki Abu Diabi a ranar 11 ga Mayu, 1986 a birnin Paris na kasar Faransa kuma dan asalin kasar Ivory Coast ne.

Daga cikin kungiyoyin da Abu Diabi ya taka leda, za mu iya ambaton Osser a Faransa, Arsenal da Marseille. Ya kuma buga wa tawagar kwallon kafar Faransa wasanni 16 na kasa. Ya yi bankwana da duniyar kwallon kafa a ranar 27 ga Fabrairu, 2019 yana da shekaru 32.