IQNA

Karatun Sayyid Mustafa Hosseini a Bait al-Zahra (AS) Kerman

Tehran (IQNA) Wani ayarin kur'ani mai tsarki da ya kunshi ma'abota Al-Kur'ani na kasar Iran sun yi tattaki zuwa birnin Kerman da ke kudancin kasar a daidai lokacin da ake cika shekaru uku da shahadar Laftanar Janar Qassem Soleimani.

Ayarin motocin na rike da da'irar kur'ani a yayin tafiyar. An shirya daya daga cikin shirye-shiryen kur'ani mai tsarki a Shahidi Soleimani Bait-ul-Zahra inda fitaccen qari Seyed Mostafa Hosseini ya karanta aya ta 95 zuwa ta 101 a cikin suratun Nisa.