IQNA

Wakilin Iran ya lashe matsayi na uku a gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Moscow

13:51 - November 21, 2022
Lambar Labari: 3488211
A yammacin ranar 20 ga watan Nuwamba ne aka kammala gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa karo na 20 a babban masallacin birnin Moscow na kasar Rasha, kuma Seyed Mustafa Hosseini dan kasar Iran ya samu matsayi na uku a wannan gasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan gasa ta fara ne a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba, inda kuma masu karatu daga kasashe 20 da suka hada da Rasha, Bahrain, Yemen, Masar, Morocco, Turkiya, UAE, Sudan, kungiyar kasashen renon Ingila da kuma Syria suka halarci gasar.

Bayan sanar da sakamakon wadannan gasa a wajen rufe gasar, Ahmed Kozo daga Turkiyya ne ya zo na daya, Abd al-Rahman Faraj daga Masar ya zo na biyu, Seyed Mustafa Hosseini ya zo na uku, sai Qari daga Yemen ya zo na hudu.

A cikin shirin za ku ga bidiyon karatun fitaccen malamin nan na Iran Sayyid Mostafa Hosseini a wajen bikin rufe wannan gasar kur'ani ta kasar Rasha.

An gudanar da wannan gasa ne bayan shafe tsawon shekaru biyu ana fama da annobar Corona, kuma an kammala a yau tare da halartar jakadun kasashen musulmi da Sheikh Ravil Ainuddin shugaban majalisar Mufti na kasar Rasha.

سید مصطفی حسینی، حائز رتبه سوم مسابقات بین‌المللی قرآن مسکو را کسب کرد

 

 

 

4101061

 

captcha