Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Sharrooq cewa, wannan aiki na ango a kasar Masar mai haske ya bai wa wadanda suka halarci bikin sha'awa.
Bayan fitar da faifan bidiyon, wasu sun taya wadannan matasa ma'aurata murna tare da bayyana cewa abin da ya fi kyau shi ne ango yana fara rayuwa da karatun ayoyin kur'ani mai girma.