A cikin bayanin da ya fitar a yau, shigaban Falastinawa ya bayyana kisan nata a matsayin wani laifi daga cikin manyan laifukan da Isra’ila take aikatawa na kisan kiyashia akan al’ummar Falastinu.
Ya ce gwamnatin Isra’ila ce ke da alhaki kai tsaye a cikin wanann danyen aiki, wadda ta bayar da umarnin kashe falastinawa ko ta wane hali.
Jami’an sojin Isra’ila dai sun kashe Shireen Abu Akleh ne a lokacin da take aikin bayar da rahoto kai tsaye a yau Laraba daga garin Jinin da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka harbe ta a kai da harsashin bindiga, daga bisani kuma ta rasu.
Lamarin dai yana ci gaba da fuskantar tofin Allah tsinwe da Allawadai daga ko’ina cikin fadin duniya.