IQNA

Jordan: An Bullo Da Sabon Tsarin Ajujuwan Koyar Da Kur'ani Mai Tsarki A Lokacin Bazara

14:43 - June 08, 2021
Lambar Labari: 3485993
Tehran (IQNA) an bullo da wani sabon tsari na bude ajujuwan koyar da kur'ani a lokacin bazara a kasar Jordan.

Shafin jaridar Anbat ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a kasar Jordan ta bayar da sanarwar cewa, ta bullo da wani sabon tsari na bude ajujuwan koyar da kur'ani a lokacin bazara a kasar.

Hussain Assaf shi ne babban daraktan cibiyar, ya bayyana cewa sun nuna wa ma'aikatar kiwon lafiya dukkanin tsare-tsaren da suka yi, kuma an amince da tsarin nasu, musamman yadda aka bayar da muhimmanci ga kula da kiwon lafiya a cikin tsarin.

Kasar Jordan na daga cikin kasashen larabawa da suke da shirye-shirye da dama na bayar da horo kan kur'ani ga yara da kuma matasa  aduk lokutan da aka yi hutun baraza, wanda a shekarar da ta gabata shirin ya fuskanci matsala saboda yaduwar cutar corona.

Shirin ya kunshi koyar da tilawa da kuma harda gami da koyar da hukunce-hukuncen karatun kur'ani wato tajwidi, da sauran ilmomi da suka shafi kur'ani.

3976145

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Jordan
captcha