IQNA

Musulmi A Kasar Kenya Sun Hada Taimako Ga Al'ummar Falastinu Mazauna Gaza

23:43 - June 07, 2021
Lambar Labari: 3485989
Tehran (IQNA) musulmin kasar Kenya hada taimako ga al'ummar yankin zirin Gaza da ke Falastinu

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, musulmin kasar Kenya sun hada taimako ga al'ummar yankin zirin Gaza sakamakon hare-haren da yahudawa suka kaddamar a yankin tare da yin barna mai yawa.

Rahoton ya ce cibiyoyi da kungiyoyin musulmi daban-daban gami da kwamitin limaman masallatan kasar, da kuma kungiyoyin bayar da agaji na musulmi da kuma bankin musulunci na kasar ta Kenya ne suka harhada taimakon.

Abubuwan da aka tara dai sun hada da abinci da kuma sauran kayayyakin bukatar rayuwa, baya ga haka kuma sun hada kudade fiye da dala miliyan biyu ta Amurka, a matsayin taimakon farko da suka fara tattara domin taimakon wadanda suka rasa kaddarorinsu da iyalansu sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza.

A tsawon kwankin da Isra'ila ta kwashe tana kaddamar da hare-hare a kan al'ummar Gaza, al'ummar musulmi na kasar Kenya har ma da wadanda ba musulmi ba, sun yi ta gudanar da zanga-zangar yin tir da Allawadai da hakan, tare da kiran al'ummar duniya da su taka wa yahudawa burki kan kisan kiyashin da suke yi kan al'ummar Falastinu.

 

3976041

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar kenya musulmin kasar Kenya taimako
captcha