Babban masallacin kasar Aljeriya wanda shi ne masallaci mafi girma a duniya, an bude shi ne a ranr 18 ga watan Oktoban 2020,a lokacin maulidin manzon Allah (SAW).
Masallacin yana fadi mita dubu 377, da hakan ya hada dukkanin bangarorinsa, baya ga wurin da ake yin salla, da kuma makekeyar haraba, akwai bangarori daban-daban a cikinsa.
Daga cikin wurare akwai makaranta da cibiyar bincike na ilimi, wanda za a iya koyar da daruruwan dalibai a lokaci guda.
Baya ga haka kuma akwai wuri na musamman da kebe domin dubar jinjirin wata tare da na'urori na zamani da aka tanada.
Hasumiyarsa wannan masalalci ita ce mafi tsawo fiye da dukkanin hasumiyoyi na masallatai a duniya baki daya, inda hasumiyar tsawonta ya kai mita 265, sannan a cikinta tana da hawa 42..
Wani abu mafi daukar hankali a ginin hasumiyar shi ne, an yi ta ne a tsarin gini irin na gargajiyar ta tsarin ginin Afirka.