IQNA

Taro A Birnin Landan Mai Taken (Imam Khomeini Malami Abin Koyi) Wanda Zai Hada Masana Musulmi Da Kiristoci

22:57 - May 30, 2021
Lambar Labari: 3485964
Tehran (IQNA) za a gudanar da zaman taro domin tunawa da zagayowar lokacin rasuwar marigayi Imam Khomeini a  birnin Landan na kasar Burtaniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar musulunci a birnin Landan na kasar Burtaniya za ta dauki nauyin shirya wani zaman taro domin tunawa da cikar shekaru 32 da  rasuwar marigayi Imam Khomeini, taron mai taken Malami Abin Koyi, wanda zai gudana a ranar Alhamis 3 ga watan yuni mai kamawa, da misalign karfe 19 zuwa 21, tare da halartar masana musulmi da kiristoci.

Daga cikin wadanda za su halarci taron Ayatollah Mahdi Hadawi Tehrani, sai Sayyid Hashem Musawi shugaban cibiyar muslunci ta birnin Lanadan, da kuma wasu masana daga kasar Jamus da kuma kasar ta Burtaniya, inda za a yi bayanai kan mahangar Imam Khomeinei a kan batutuwa daban-daban ta fuskar ilimi.

Wadanda suke bukatar shiga taron ta hanyar yanar gizo za su iya shiga ta wannan adireshi domin yin rijistar sunayensu:

https://ic-el.uk/events/a-seminar-on-the-۳۲nd-anniversary-of-the-passing-away-of-imam-khomeinis-r-a

 

3974425

 

 

 

 

captcha