IQNA

Taro Kan Kur’ani Karo Na 114 Da Cibiyar Ahlul Bait (AS) Take Shiryawa

23:52 - April 13, 2021
Lambar Labari: 3485803
Tehran (IQNA) za a gudanar da taro kan kur’ani mai tsarki karo na 114 wanda cibiyar Ahlul bait (AS) take daukar nauyin shiryawa.

Cibiyar Ahlul bait (AS) ta sanar da cewa, za ta gudanar da taro kan kur’ani mai tsarki karo na 114 wanda take daukar nauyin shiryawa wanda kuma yake samun daruruwan mahalrta daga sass ana duniya.

Yanzu haka dai an bude shafi na yanar gizo na wannan taro ga wadanda suke son shiga ciki, kasantuwar cewa taron zai gudana ne ta hanyar yanar gizo, ga adireshin shafin kamar haka: www.114award.ir .

Daga cikina bubuwan da masu bukatar shiga wannan taro da kuma gasar da za a gudanar a cikinsa, za su iya tanadar wasu abubuwa da za su nuan da suka shafi kur’ani, kamar wasu ayyukan da suka gudanar da suka shafi kur’ani.

Mataimakin shugaban cibiyar Ahlul bait ta duniya Hojjatol Islam Muhamamd Jawad Zari’an ya bayyana cewa, yanzu haka ana yin rijistar sunayen wadanda za su shiga wannan gasa har zuwa cikin wata mai kamawa.

Ya ce babbar manufar wannan taro da kuma gasar da ake gudanarwa ita ce kara kara yada da kuma fadada lamarin kur’ani mai tsarki a duniya, domin kuwa kur’ani ya kunshi ilimi mai fadi wanda har kullum kara gano abubuwa na ilimi ake yi a cikin kur’ani mai tsarki.

A kan haka ya ce dukkanin wadanda suke da bukatar nuna wasu abubuwa na ilimi daga kur’ani ko kuam wasu ayyuka na fasaha da suka shafi kur’ani, kamar fasahar rubutun ayoyi da ake kayatawa da salo daban-daban, duk za su iya shiga cikin shirin.

Haka nan kuma ya bayyana cewa za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda aka zabi ayyukansu a matsayin wadabda suka zo an daya da na biyu da kuma na uku.

3963507

 

captcha