IQNA

Mabiya Mazhabar Ahlul Bait (AS) A Ghana Suna Bayar Da Tallafi Ga Asibitocin Kula Da Masu Larura Ta Musamman 

20:35 - March 09, 2021
Lambar Labari: 3485730
Tehran (IQNA) mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) a kasar Ghana sun bayar da tallafin ga wasu asibitocin kula da masu larurar tabin hankali.

Jaridar Graphic Ghna ta bayar da rahoton cewa, a jiya Litinin cibiyar Imam Baqir (AS) ta mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) a kasar Ghana sun bayar da tallafin ga wasu asibitocin kula da masu larurar tabin hankali a wasu biranan kasar.

Rahoton ya ci gaba da cewa, Sheikh Sulaiman Nadi Bamba shugaban cibiyar, shi ne ya jagoranci raba wadannan kayayyakin tallafi, da suka hada da ruwan sha, abinci, sabullai na wanka da wanki, man girki, sukari da dai sauransu.

Ya ce wannan koyarwa ce irin ta addinin muslunci, kuma wannan shi ne abin da manzon Allah (SAW) ya yi kuma ya koyar da musulmi, wato ayyukan alhairi da jin kai ga bil adama.

Malamin ya kara da cewa, ba za su taba ja da baya ba ko nuna gazawa wajen ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka, wanda kuma hakan yana zuwa ne a lokacin da ake bukatar irin wannan taimako, wato lokacin fuskantar annobar corona.

3958490

 

captcha