IQNA

Maratnin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ga Faransa

23:50 - May 29, 2020
Lambar Labari: 3484846
Tehra (IQNA) Kakakin ma’aikar harkokin wajen Iran ya mayar wa ministan harkokin wajen kasar Faransa da martani, kan hukuncin da kotu a Iran ta yanke a kan wata ba’iraniya mai  takardun zama ‘yar kasar Faransa.

Kakakin ma’aikar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya mayar wa ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian da martani, dangane da furucin da ya yi kan hukuncin da wata kotu a Iran ta yanke a kan wata ba’iraniya, na daurin shekaru 5, wadda take dauke da takardun zama ‘yar kasar Faransa.

A wata zantawarsa da wani gidan radiyo a kasar Faransa, ministan harkokin wajen kasar ta Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana cewa, yanke hukuncin dauri a kan ba’iraniyar da ke dauke da takardun zama ‘yar kasar Faransa da kotun Iran ta yi, ya jefa alakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu cikin mawuyacin hali, inda ya ce hukuncin na siyasa ne, kuma yana kira ga Iran da ta gagaguta sakin matar.

Musawi ya ce ministan harkokin wajen Faransa ba shi da hakkin bayar da umarni ga kotun kasar Iran, domin kuwa bangaren shari’a akasar yana cin gishin kansa ne, kuma an yanke hukunci kan matar ne bayan samun ta da aikata laifuka da suka shafi tsaron kasa, wanda kuma babu wata kasa ta duniya da za ta amince da hakan.

Ya ce bayan yanke wannan hukunci, lauyan ya matar ya tabbatar da cewa a kan zargin aikata laifi da ya shafin tsaron kasa ne aka daure ta, a kan haka bisa ga dokokin kasar ta Iran, matar tana da hakkin daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci, kamar yadda dokar shari’a a kasar ta tanada.

 

 

3901623

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kakakin
captcha