IQNA

A Mako Mai Zuwa Kwamitin Tsaro Zai Gudanar Da Zama

23:56 - April 26, 2020
Lambar Labari: 3484748
Tehran (IQNA) a mako mai zuwa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai gudanar da zama kan batun corona.

Jaridar Quds Arabi ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya sun tabbatar da cewa  amako mai zuwa ne kwamitin zai gudanar da zama domin fitar da kuduri kan halin da ake ciki na matsalar corona.

Tun sama da makonni biyu da suka gabata ne kwamitin tsaron ya gudanar da zama wanda Jamus ta kira, domin tattauna batun na corona da kuma daukar matakai, amma saboda sabanin da ke akwai tsakanin Amurka da kuma China da Rasha a daya bangaren, an kasa cimma matsaya kan batun.

A halin yanzu dai kwamitin zai gudanar da zama domin tattauna daftarin kudirin da Faransa da Tunisia suka gabatar ne, kan dakatar da tashe-tashen hankula  aduniya, tare da mayar da hankali ga yaki da cutar corona.

Ana sa ran cewa, idan dukkanin mammbobin kwamitin suka suka cimma daidaito kan wannan batu za su fitar da kudiri kan hakan.

3894323

 

 

 

 

captcha