Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na News ya nakalto daga ma’ikatar tsaron kasar Faransa cewa, an halaka daya daga cikin jagororin wata kungiyar ‘yan ta’adda a Mali mai suna Suna Nusrat Islam wal Muslimin.
Bayanin ya ce an kai wani hari ne kan ‘yan ta’addan ne a ranar 9 ga watan Oktoba inda aka halaka Ali Maichu.
Wannan kungiya dai tana kaddamar da hare-hare kan sojojin kasar Mali da na majalisar dinkin duniya da kuma na kasar Faransa.
Majalisar dinkin duniya ta ce Maichu yana da alakada Daesh da kuma alkaida, a kan haka aka saka sunansa cikin wadanda ake nema.