IQNA

Za AGudanar Da Taro kan Kare hakkokin Al'umma Palastine A Uganda

23:56 - May 25, 2019
Lambar Labari: 3483673
Bangaren kasa da kasa, a ranar laraba mai zuwa za a gudanar da zaman taro mai take kare hakkokin al'ummar palastinu, wanda zai gudana a kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, fiye da mutane 70 da suka hda da masaa da malamai da fitattun 'yan siyasa ne a na kasar ganda aka gayyata domin halattar taron.

A cikin taron kuma za a yi dubi kan irin gagaumar gudunmawar da marigayi Imam Khomeni ya bayar wajen karfafa hada kan al'ummar musulmi, wanda dukkanin raunin da musulmi suka samu da tarwatsewar da suka yi , yana da alaka ne da rashin hadin kansu.

Za a gabatar da makaloli daga masana da malaman addini da kuma malamn jami'io, kamar tadda kuma tashar tv salam za ta watsa shirin kai tsaye.

 

3814495

 

 

captcha