Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Karim Mansuri makarancin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran ya gabatar da karatu a kasar Ghana kasar da tun kwanaki 10 yake ziyartarta.
Ya gabatar da karatu a wurare daban-daban na kasar tare da halartar musulmi a cikin wanann wata na Ramadan.
A jiya ma gabatar da karatun kur’ani mai tsarki Husainiyar mutanen Lebanon da ke birnin Accra fadar mulkin kasar, inda ya karanta ayoyi na 4 da 5 a cikin surat Yusuf ayoyin da ke cewa ( A lokacin da Yusuf ya ce ya babana ni na yi mafarki naga taurari goma sha daya da rana da wata na gan su suna yi mani sujada) ( yace kada ka bayyana mafarkinka ga ‘yan uwanka sai shirya maka makirci, hakika shi shaidan makiyin mutum ne mabayyani).
Za a iya duba faidan bidiyon tilawar a nan: