IQNA

Matsayar Da Trump Ya Dauka Kan Batun Tuddan Golan Ta Saba Wa Ka'ida

23:38 - March 23, 2019
Lambar Labari: 3483484
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta sanar da cewa, amincewar da Trump ya yi da tuddan Golan na Syria a matsayin mallakin Isra'ila, ya saba wa dukkanin dokoki na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A cikin bayanin da ta fitar a yau, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta mayar da kakkausan martani kan matsayar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na amincewa da tuddan Goland na kasar Syria da Isra'ila ta mamaye, a matsayin mallakin Isra'ila a hukumance.

Bayanin ya ce tun bayan da Isra'ila ta mamaye wadannan tuddai na Syria, babu wata kasa ta duniya da ta amince da su a  matsayin mallakin Isra'ila, kamar yadda hatta majalisar dinkin duniya ba ta amince da wadannan tuddai  a matsayin mallakin Isra'ila ba, inda majalisar dinikin duniya a hukumance take saka tuddan Golan a cikin yankunan Syria.

A kan haka ma'ikatar harkokin wajen kasar ta Iraki ta ce ba ta amince da wannan matsaya ba, kuma tana yin Allawadai da hakan, tare da jaddada cewa Tiddan Golan mallakin Syria ne bisa dokoki na kasa da kasa.

Ita ma  a nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta sanar da cewa ba ta amince da matakin na Trump ba, kamar yadda ita gwamnatin kasar Rasha ta fitar da bayani, wanda a cikinsa ta yi watsi da wannan matsaya ta gwamnatin Amurka.

3799519

 

 

captcha