IQNA

Burkina Faso: An Gudanar Da Zaman Taro mai Taken Matsayin Mata A Musulunci

23:47 - March 18, 2019
Lambar Labari: 3483470
An gudanar da wani zaman taro mai taken matsayin mata a cikin adddinin musulunci a kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da zaman taro kan matsayin mata a cikin addinin muslunci a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso.

Rahoton ya ce an shirya taron ne da nufin kara bayyana matsayin addinin muslucni kan yadda ake take hakkokin mata a cikin lamurra da dama da suka shafi rayuwar zamantakewar al’umma.

Manyan malaman addini da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar sun halarci wurin taron, haka nan kuma cikin wadanda suka gabatar da jawabi akwai Sheikh Abdullahi Bawi wakilin jami’ar Amustafa a kasar ta Burkina Faso.

Taron wanda aka nuna a kafofin yada labarai na kasar ya samu karbuwa daga bangarori daban-daban na mabiya addinai a kasar ta Burkina Faso musulmi da wadanda ba musulmi ba.

3798627

captcha