Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, wasu ‘yan bindiga sun sace sheikh Ahmad Sulaiman wani faitaccen malamin kur’ani a Najeriya a ranar Alhamis da ta gabata, a lokacin da yake bi hanyar Kankara a cikin jahar Katsina bayan dawowa daga tafiya a jahar Kebbi.
Rahoton ya ce an sace malamin ne tare da wasu mutane biyar ad suke tare das hi, bayan da suka halarci wani taron karatun kur’ani a tsarki a jahar Kebbi da ke arewacin Najeriya.
Bayanin ya kara da cewa sau tari ‘yan bindigar sukan nenmi kudaden fansa nea duk lokacin da suka kame mutane suka yi garkuwa da su, musammana lokacin da suka kame fitattun mutane sukan karbi kudade masu tarin yawa, tare da yin barazanar kashe su matukar ba a ba su kudi da yawa ba.