Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin da ke saka kayan tarihi domin tallarsu a yanar gizo Jelly Fish Tree ya sanar da cewa, an sanya wannan kwafin kur’ani da aka tarjama a shekarar 1649 a kasuwa domin fansar da shi.
Wannan shafi dai na kasar Afirka ta kudu ne, kuma yak an saka tallar abubuwa masu kima da tarihi ne kawai domin sayar da su.
Yanzu haka dai kima ta farko da aka sanya wa wannan kur’ani shi ne dala dubu 800.