IQNA

An Gina Masallaci A Wurin Shakata A Afrika Ta Kudu

23:56 - December 04, 2018
Lambar Labari: 3483180
Bangaren kasa da kasa, an gina masallaci a wani babban wurin shakatawa a kasar Afrika ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na iol ya bayar da rahoton cewa, a jika aka bude masallaci a wani babban wurin shakatawa a garin Skukuza da ke arewacin kasar Afrika ta kudu.

An gabatar da shawarbude wannan masallaci ne tuna  cikin shekara ta 2009, amma sai yanzu aka aiwatar da hakan.

Mai’aikatar kula da wuraren shakatawa ta kasar Afrika ta kudu ta sanar da cewa, muuslmin kasar sun agaza, inda suka tara wasu kudade domin gina wannan masallaci.

Akwai muuslmi fiye da miliyan daya a kasar Afrika ta kudu, wanda hakan nufin cewa adadinsu ya kai kashi biyu cikin dari na mutanben kasar.

3769502

 

 

 

 

 

captcha