IQNA

Dakarun Aljeriya Sun Fara Kaddamar Da Farmaki Da Nufin Kame Jagoran Alqaeda

23:52 - September 13, 2018
Lambar Labari: 3482980
Bangaren kasa da kasa, dakarun kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda ayankin Magrib.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin DMCA ya bayar da rahoton cewa, dakarun sojion kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki a cikin tsaunukan Buwairah da ke tazarar kilomita 120 daga a gabashin birnin Algiers, da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda  ayankin Magrib Abdulmalik Durkidal.

An haifi Durkidal a kasar Aljeriya ne a cikin shekara ta 1971, ya kuma halarci kasar Afghanistan inda ya yi yaki tare da kungiyoyin wahabiyawa masu tsatsauran ra'ayi.

A cikin shekara ta 2004 ya dawo Aljeriya ya zama jagoran kungiyar Salafiyya mmai tsatsauran ra'ayi a  kasar, a cikin shekara ta 2006 ya zama jagoran kungiyar alqaeda  a yankin.

Ana sa ran a wanna karon farmakin da aka fara kaddamarwa da nufin kame shi zai bayar da damar halaka shi ko kua kamshe tare da daruruwan 'yan ta'adda da suke tare da shi.

3746510

 

captcha