IQNA

Fiye Da ‘Yan Ci Rani Dubu Ne Suka Mutu A Gabar Ruwan Libya A Cikin 2018

23:10 - June 23, 2018
Lambar Labari: 3482783
Bangaren kasa da kasa, Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan halakar bakin haure kimani dari biyu da ashirin a gabar tekun a kasar Libya a cikin yan kwanakin da suka gabata.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majiyar hukmar tana fadar haka a yau Jumma'a ta kuma kara da cewa a ranar Talatan da ta gabata bakin haure dari ne suka nutse a gaban tekun kasar ta Libya amma mutum biyar kacal suka tsira da ransu, sai kuma a rannan wata kwalekwalen ta zubar da bakin haure dari da talatin a cikin tekun inda mutane saba’in suka rasa rayukansu.

A wani labarin wasu bakin hauren da aka ceto daga halaka sun bayyana cewa akwai wasu mutane kimani hamsin tare da su da suka nutse a cikin teku. 

 A Nata bangaren hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniyar ta nuna damuwarta kan yawan bakin hauren da suka halaka a tekun da medeteranian, sannan ta bukaci kasashen duniya da kuma kungiyoyin bada agaji na gwamnatoci da masu zaman kansu su tashi tsaye don kawo karshen mutuwar da bakin hauren suke yi a cikin tekun Medeteranian.

Tun daga lokacin da kasashen turai suka jagoranci kungiyoyi masu ra’ayin alkaida wajen kifar da gwamnatin Gaddafi tare da yi masa kisan gilla a cikin shekara ta 2011, har yanzu kasar Libya bata kara samun zaman lafiya ba.

3724424

 

captcha